NNPC ya goyi bayan Tinubu kan cire tallafin man fetur

0
155

Kamfanin Man Fetur na Kasa (NNPCL), ya yi maraba da sanarwar da shugaba Bola Tinubu ya yi kan cire tallafin man fetur.

Shugaban kasar, a jawabinsa na farko a ranar Litinin, ya bayyana aniyar kawo karshen biyan tallafin, inda ya bayyana cewa kasafin kudin 2023 bai yi tanadin tallafin ba, don haka karin biyan kudin bai dace ba.

Da yake tsokaci a wani taron manema labarai a ofishin NNPC da ke Abuja, NNPC ya shaida wa ’yan Najeriya cewa matakin zai amfani kowa da kowa.

A cewar shugaban kamfanin, Mele Kyari, kamfanin yana kashe makudan kudaden ribar da ya samu wajen tallafin man da ake biya.

Sai dai Kyari ya ce babu bukatar damuwa saboda layin man fetur a wasu yankunan Babban Birnin Tarayya Abuja.

Ya kara da cewa, kamfanin na da isasshen mai da zai wadaci kasar nan na tsawon kwanaki 30 masu zuwa.

Ya kara da cewa NNPCL yana sa ido kan yadda gidajen mai ke rarraba man a fadin kasar nan.

Kyari ya yi maraba da matakin da shugaban kasa Bola Tinubu ya dauka na cire tallafin man fetur da kuma tabbatar wa ’yan Najeriya isassun albarkatun man fetur da ake da su a fadin kasar nan.

A lokacin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, Gwamnatin Tarayya ta bayyana a watan Janairu cewa za ta dakatar da biyan tallafin man fetur a karshen watan Yuni.

Ministar kudi, kasafi da tsare-tsare a lokacin, Zainab Ahmed, ta bayyana cewa a cikin kasafin kudin 2023, gwamnati ta yi tanadin Naira tiriliyan 3.36 don biyan tallafin man fetur domin cika watanni shida na farkon wannan shekara.

Ta ce hakan ya yi daidai da tsawaita wa’adin watanni 18 da aka sanar a farkon shekarar 2022.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here