Ba ma kokarin musuluntar da Nijeriya –Shettima

0
130

Zababben mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya yi watsi da jita-jitar da ake yadawa cewar shugaban kasa mai jiran gado, Bola Ahmed Tinubu yana kokarin Musuluntar da Nijeriya.

Ya bayyana haka ne a yayin wani taron lacca ta musamman da aka gudanar a Abuja ranar Asabar gabanin rantsar da sabuwar gwamnati.

“Asiwaju Bola Ahmed Tinubu Musulmi ne wanda yake auren Kirista, ba wai Kirista kadai ba, amma fasto a Cocin Redeem.

“Mutumin da bai Musuluntar da iyalinsa ba, mutane suna cewa yana son ya Musuluntar da kasa baki daya,” in ji Kashim Shettima.

Shettima ya kuma bayyana cewa a lokacin yana gwamnan Borno, akwai coci da dama da Boko Haram suka kone, bayan ya yi yunkurin gyaran cocin an ba shi shawara kada ya kuskura ya sake gina cocin.

“Na shaida wa mutanen Borno cewa Kiristoci su ma suna da ruwa da tsaki a Nijeriya, ‘yan uwana ne maza da mata, na yi gaban kaina na sake gina wadannan coci-cocin,” in ji shi.

A yayin taron, Kashim Shettima ya bayyana cewa da gangan ya dauki dan kabilar Igbo kuma mai bin darikar Katolika domin ya zama shugaban masu tsaronsa.

Kazalika ya ce ya zabi Kirista daga arewacin Nijeriya domin ya zama dogarinsa don kara hadin kan kasa.

A lokacin da yake bayani, Kashim Shettima ya bukaci jami’an tsaron biyu su mike tsaye domin mutane su tabbatar da hakan inda aka yi ta tafi da sowa.

Tun kafin a gudanar da zaben 2023, an sha sukar Jam’iyyar APC mai mulki kan hadin da ta yi na Musulmi da Musulmi a matsayin wadanda za su yi takarar shugaban kasa da mataimaki inda ake cewa bai kamata ba domin Nijeriya ba ta Musulmai ba ce kadai.

Sai dai jam’iyyar ta sha kare zargin da ake yi mata inda ta rika jaddada cewa ta dauki matakin ne bisa cancanta ba addini ko yankin da mutanen suka fito ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here