Ƙalubalen da ke gaban sabon gwamnan Kano

0
115

Jihar Kano na ɗaya daga cikin jihohin da jam’iyyar adawa za ta karɓi mulki daga jam’iyyar APC, bayan hukumar zaɓe ta ayyana Abba Kabir Yusuf, na NNPP, a matsayin wanda ya lashe zaɓen na watan Maris.

Kamar kowace jiha a Najeriya, Kano na da nata matsalolin kuma hankalin al’ummar jihar ya karkata kan zaɓaɓɓen gwamnan Abba Kabir Yusuf, wanda za a rantsar a ranar 29 ga watan Mayu domin ganin salon mulkinsa da kuma ƙoƙarin da zai yi wajen magance matsalolin.

Ko waɗanne ƙalubale ke gaban Abba Gida-Gida?

Kabiru Sa’id Dakata, babban daraktan cibiyar wayar da kan al’umma a kan shugabanci na gari da tabbatar da adalci, CAJA, ya ce Abba Kabir, ya zama gwamna ne a “doro na tafiyar Kwankwasiyya” wadda matasa suka san ta kan bayar da ilimi kyauta ba wai iya matakin firamare da sakandare ba har ma jami’a a ciki da wajen Najeriya.

Masanin ya bayyana wasu daga cikin manyan ƙalubalen da Abba Kabir Yusuf, zai fuskanta.

Ƙalubalen kuɗi

Kabiru Dakata, ya ce zaɓaɓɓen gwamnan zai shiga gwamnati ne a lokacin da lalitar gwamnatin ke fama da rashin kuɗi, abin da ya ce babban ƙalubale ne domin “su matasa da za su amfana da wannan abu, burinsu shi ne daga fara aikin gwamnati, za a fara aiwatar da tsarin na ilimi kyauta.”

Ya ce rashin kuɗi na iya kawo tarnaƙi wajen cika tsammanin matasa na ganin sabon gwamnan ya yi koyi da tsarin bayar da ilimi kyauta tun daga firamare har zuwa jami’a.

Biyan Basuka

Kabiru Dakata, ya ce ƙalubalen tulin bashin da ya yi wa gwamnatin Kano katutu wani lamari ne babba kasancewar basuka ne da ake bin jiha.

“Basussuka ne da aka yi wanda yarjejeniyarsu ta tanadi lokaci da za a biya”. in ji Dakata.

Ya bayar da misali da wasu basukan da aka ƙayyade a biya cikin kowanne wata sannan lokacin biyan basukan bai ƙare ba.

A cewarsa, gwamnan zai zo ne ya fara tunkarar yadda zai biya ma’aikata albashi da kuɗaɗen da zai aiwatar da ayyukan more rayuwa da kuɗaɗen da zai biya basussukan.

Karɓo filayen da aka sayar

Ƙarin ƙalubalen da Kabiru Dakata ya ce gwamnan na Kano zai fuskanta shi ne batun sayar da filaye da wurare masu muhimmanci da gwamnati bai barin Kano ta yi ba bisa ƙa’ida ba.

Ya ce akasarin kadarorin na wuraren ci gaban al’umma ne kamar makarantu da asibitoci.

Kabiru Dakata ya bayar da misali da yadda aka sayar da ɓangaren asibitin Nasarawa da aka sayar wa makusantan gwamnan.

A cewarsa, gwamnan zai zo ne a yayin da yake neman yi wa jama’a ayyukan da za su mora a gefe guda kuma, yana ƙoƙarin yin duk yadda za a yi domin ganin kadarorin da aka sayar an maida wa gwamnati – wani batu da wataƙila sai an kai ga zuwa kotu.

Ya ƙara da cewa ba wai iya filaye bane aka yi gwanjonsu, har ma da fitulun kan titi da aka sayar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here