Abba Kabir Yusuf ya gayyaci Muhammadu Sanusi II bikin rantsar da shi

0
136

Gwamnan Kano mai jiran gado Abba Kabir Yusuf ya gayyaci Muhammadu Sanusi II bikin rantsar da shi a Kano.

Za a yi bikin ne ranar 29 ga Mayu a filin wasa na Sani Abacha a Kano.

“Ina gayyatarka bikin rantsar da ni da mataimakina Kwamred Aminu Abdusslam Gwarzo.”

“Kasancewarka a wajen bikin ba wai zai kayatar ba ne kawai amma zai kasance muhimmin cigaba da goyon baya gare mu,” kamar yadda gwamnan mai jiran gado Abba Kabir Yusuf ya bayyana a cikin takardar gayyata da ke ɗauke da sa hannunsa.

Sunusi Bature Dawakin Tofa, kakakin gwamnan Kano mai jiran gado, ya tabbatar wa BBC cewa ba wai Muhammadu Sanusi II kawai aka gayyata bikin rantsar da sabon gwamnan na Kano ba, an kuma gayyaci Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, jagoran NNPP da Aliko Dangote da Abdul Samad Isyaka Rabiu da wasu manyan mutane na Najeriya da   ƙasashen waje.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here