“’Yan Najeriya da kansu za su roki Tinubu ya yi tazarce”

0
113

Shugabar Mata ta Jam’iyyar APC, Betta Edu, ta ce shugaban kasa mai jiran gado Bola Tinubu zai yi wa ’yan Najeriya ayyukan da har su da kansu za su koma rokon sa ya yi wa’adi na biyu.

Betta Edu ta bayyana cewa a halin yanzu, Tinubu ya riga ya tsara abubuwan da yake son cin nasara a kansu cikin kwana 60 na farkon mulkinsa, daga ranar Litinin, 29 ga watan Mayu da muke ciki.

Ta ce shugaban kasa mai jiran gadon ya riga ya shirya cike wuraren da aka samu nakasu a gwamnatin Shugaba Buhari mai barin gado kuma zai fara aiwatar da ayyuka ne daga ranar da aka rantsar da shi.

“Zan iya rantse muku cewa ’yan Najeriya da kansu za su roki Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya dawo ya yi wa’adin mulki na biyu.

“Ya kamata a fahimci cewa Najeriya ci gaba take ba ta tsayawa, kuma idan aka saurari jawaban Shugaba Buhari da kyau, za a ji yadda yake bayyana irin rawar ganin da ya taka.

“Ya kuma jaddada cewa zai mika kasar ga  hannun mutumin da ya yi amanna zai ci gaba daga wurin da ya tsaya kuma zai yi aiki fiye da wanda ya yi,” in ji ta a wata hirar talabijin da tashar Channels.

Shugabar matan ta APC ta ci gaba da cewa, “Duk wanda ya zauna da Asiwaju Bola Tinubu ya san mutum ne mai zurfin tunani da kuma zartar da aiki; ga shi kuma da basira wajen nazari da tsara abubuwa.

“Zan iya bugun kirji cewa Tinubu ya riga ya gama tsara abubuwan da zai yi a ckin kwana 60 na farko —  da abubuwan da ake son cimma da hanyoyin da za abi da kuma inda aka dosa.

“Yana da cikakken sani game da aikin da ke gabansa kuma ya riga ya shirya, lokaci kawai yake jira ’yan Najeriya fara gani a kasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here