Rancen Paris Club: Gwamnati za ta dawo wa jihohi kudadensu

0
103

Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF) mai barin gado, Gwamna Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na Jihar Sakkwato, ya sanar cewa Gwamnatin Tarayya ta amince da daina cirar kudade daga asusun jihohi da na kananan hukumomi domin biyan rancen London Paris Club.

A yayin zaman gaggawa karo na 7 da kungiyar ta gudanar a daren Talata, Tambuwal ya sanar da takwarorinsa cewa Ministar Kudi ta amince da bukatar kungiyar ta dawo wa gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi  a  kudaden da aka cira a baya sa sunan rancen.

Tambuwal ya kara da cewa kungiyar ta nada Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq na Jihar Kwara a matsayin sabon shugaban da zai jagorance ta, da kuma Gwamna Seyi Makinde na Jihar Oyo a matsayin mataimakinsa.

Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq zai maye gurbin Tambuwal, wanda wa’adinsa ke karewa ranar Litinin 29 ga watan Mayu da muke ciki.

“Mambobin kungiyar sun gamsu da nasarorin da aka samu wajen kaddamar da sabbin gwamnoni da wadanda suka yi tazarce, wanda aka gudanar daga 14 zuwa 19 ga watan Mayu, 2023,” in ji  Tambuwal.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here