Tarin Basussuka: Ayyukan more rayuwa muka yi ba almundahana ba – Buhari

0
119

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata a Abuja ya bayyana cewa samar da ayyuka da ababen more rayuwa na daga cikin muhimman abubuwan da ya fi mayar da hankali a gwamnatinsa domin samar da hanyoyin arziki da kuma rage radadin talauci.

Da yake jawabi a taron kaddamar da gadoji uku, sakatarori uku da kuma aikin hanya daya da gwamnatinsa ta gudanar, shugaban kasar a wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu ya fitar, ya kare sukar da ake yi wa gwamnatinsa na amso basussuka inda ya ce “Duk aikin da muka yi na more rayuwar jama’a ne, mun yi su ne muna sane kuma cikin shiri ba bagtatan abun ya fado mana ba. Mun yi ayyukan ne muna sane don kirkirar wani abu da za mu yaki talauci da shi kuma mu samar da ci gaban tattalin arziki da samar da ayyukan yi da bude hanyar arziki ga jama’armu.”

Ya jaddada cewa, shi ma yana sane da damuwar ‘yan Nijeriya kan basussukan da gwamnatinsa ta amso, amma kudin an zuba su ne duka acikin ayyukan da kowa na iya ganinsu da idanunsa.

Ya kara da cewa, ana iya gane karfin tattalin arzikin sauran kasashe ta hanyar lura da hannun jarinsu acikin ababen more rayuwa da suka zuba a kasar, wanda watakila da basussuka suka yi gine-ginen.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here