Direba ya murkushe ’yan uwan juna 4 har lahira a Jigawa

0
114

Wani direban motar haya ya murkushe mutum hudu ’yan uwan juna har lahira a Karamar Hukumar Babura ta Jihar Jigawa.

Wani mazaunin garin ya shaida wa Aminiya cewa lamarin ya faru ne a yammacin ranar Lahadi, inda wata mota ta bugi babur din da mutanen ke kai, inda duk suka mutu nan take.

Kakakin hukumar tsaron farin kaya (NSCDC) a Jihar Jigawa ya tabbatar da faruwar lamarin, a wata sanarwa da ya fitar.

A cewarsa: “Mummunan hatsari ya auku ne a jiya, Lahadi, 21 ga watan Mayu, da misalin karfe 5 na yamma a cikin garin Babura, daura da hanyar Babura zuwa Gumel, kuma mutane hudu sun mutu nan take.”

Lamarin ya faru ne a lokacin da direban motar hayar ke tafiya zuwa Gumel cikin sauri ya afkawa wadanda lamarin ya rutsa da su a kan babur a hanyar kauyensu mai suna Kolori.

Wadanda suka rasa rayukansu sun hada da Gambo Mutari mai shekara 45 da matarsa Fiddausi Abdullah mai shekaru 2a da kuma surukarsa Hauwa Maigari da yaronsu mai shekara biyu kacal.

An garzaya da su babban asibitin Babura wanda kuma aka tabbatar da mutuwarsu.

An yi jana’izarsu kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here