Abubuwa shida kan sabuwar matatar man fetur ta Ɗangote

0
120

A ranar Litinin ɗinnan Shugaban Najeriya Muhammdu Buhari ke ƙaddamar da matatar mai ta Dangote, wadda ke da ƙarfin tace mai ganga dubu 650 a rana.

Shugaban matatar, Sanjay Gupta ya ce matatar ita ce irinta mafi girma a duniya.

Wasu masana na cewa matatar za ta samar da ayyukan yi ga mutane da dama a Najeriya.

Kuma za ta samar da abubuwa kamar man fetur (PMS) da man dizil (AGO) da man jirgin sama da kalanzir da ma wasu abubuwan da dama.

Bayani kan matatar

  • An gina matatar ne a yankin Ibeju-Lekki na jihar Lagos a filin da ya kai fadin eka 2,635.
  • Bayanai daga rukunin kamfanonin Dangote sun ce matatar ita ce irinta mafi girma a duniya inda za ta rinƙa tace ganga 650,000 ta ɗanyen mai.
  • Idan ta fara aiki ɗari bisa ɗari za ta iya tace duk man fetur da ake buƙata a Najeriya har ma a samu rara da za a fitar zuwa wasu ƙasashe a kullum.
  • An tsara ta yadda za ta iya sarrafa nau’uka daban-daban na ɗanyen mai daga ƙasashen Afirka da na ƙasashen Gabas ta tsakiya da yankin Amurka.
  • Matatar tana da manyan tankuna 177 waɗanda za su iya ɗaukar mai da yawansa ya kai lita biliyan 4.742.
  • Wani bayani da rukunin kamfanonin Dangote ya fitar ya ce an yi amfani da na’urorin yashe ƙasa mafiya girma a duniya, inda aka yashe ƙasa mai yawan gaske a wurin, aka kuma kashe kuɗi kimanin yuro miliyan 300 a aikin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here