An kwashe wa Juventus maki 10 a Serie A

0
112

An kwashe wa Juventus maki 10, bayan bincike da ake yi kan yadda kungiyar ta yi cinikin ‘yan kwallo a baya.

Tun a cikin watan Janairu aka kwashe mata maki 15, amma wata kotun daukaka kararrakin wasanni a Italiya ta soke hukuncin a Afirilu, amma ta bukaci a sake bibiyar lamarin.

An bayar da sanarwar wannan hukuncin ranar Litinin, kafin wasan da Juventus za ta kara da Empoli a Serie A.

Da wannan hukuncin Juventus ta yi kasa zuwa ta bakwai a teburin Serie A, kenan ta fice daga gurbin masu buga gasar zakarun Turai ta badi

Napoli ce ta lashe kofin babbar gasar tamaula ta Italiya na bana, tun kan sanar da wannun hukuncin ta bai wa Juventus ta biyu a teburi tazarar maki 17.

Idan Juventus ta doke Empoli ranar Litinin za ta koma ta biyar da tazarar maki biyu a kasan AC Milan, wadda ita ce a gurbi na hudu a Champions League a badi.

Kamar yadda aka wallafa a wasu kafar yada labarai a Italiya na cewar babbar kotu za ta saurari batun ranar 26 ga watan Oktoba don fayyace ko za a gurfanar da kungiyar a Turin.

Da kuma tabbatar da ko an yi binciken kungiyar a Milan ko kuma a Rum.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here