Shawarar da shugabar cibiyar kasuwanci ta duniya ta bai wa sabbin gwamnoni

0
93

Darakta Janar ta Cibiyar Kaswuanci ta Duniya (WTO), Dakta Ngozi Okonjo-Iweala, ta shawarci gwamnonin Nieriya su kaucewa rungumar bashi a jihohinsu maimakon haka ya kamata su rungumi bunkasa jin dadin rayuwar al’umma jihar su in har suna son samun nasara a mulkinsu.

Ta bayyana haka ne a cikin jawabin da ta gabatar a taron gwamnoni masu barin gado da masu kamawa wanda kungiyar gwamnonin Nijeriya ta shirya da aka kuma yi a fadar shugaban kasa da ke Abuja ranar Litinin. Ta nuna muhimmancin tafiyar da harkar kudaden gwamnati yadda ya kamata tare da bukatar tabbatar da ci gaba da biyan albashin ma’aikata, wannan zai haifarda kwanciyar hankali a jihohi.

Okonjo Iweala wadda ta taba rike mukamin ministar kudi a zamanin mulkin Obasanjo da Jonathan ta kuma bukaci gwamnonin su muhimmanntar da biyan albashin malaman makarantu, ma’aikatan lafiya, su kuma zuba jari a bangaren ilmi, kiwon lafiya da sauransu.

Ta kuma nemi su karfafa hanyoyin samun kudin shiga, ta ce, akwai bukatar gwamnoni su rika buga bayanan kudaden da ke shigo musu na haraji a kafafen watsa labarai don al’umma su rika sanin yadda ake kashe kudaden jihar.

Ta kuma kara a cewa, yana da matukar muhimmanci, gwamnoni su lura da basukan da ke kansu su kuma zuba jari a bangaren ilimi, kiwon lafiya da sauransu, a kan haka ta nemi gwamnonin su samar da yanayi mai tsafta wanda zai jawo hankulan masu zuba jari daga ciki da wajen kasa, don a halin yanzu ya kamata Nijeriya ta sanya kanta a matsayin kasa mai sarrafa kayayyaki a yankinmu na Afrika dama duniya baki daya.

Ta kuma nemi Gwmanoni su bunkasa jihohinsu ta yadda matasa masu son fita wasu kasashen waje cirani za su zauna.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here