Ba ni na fara sayar da gidajen gwamnati ba – Ganduje

0
150
Ganduje
Ganduje
Gwamnan jihar Kano da ke Najeriya Abdullahi Umar Ganduje yace ba shi ya fara sayar da gidajen gwamnati ba, saboda haka bai ga dalilin korafi akai ba. 

Yayin da ya ke mayar da martani akan irin korafe korafen da suka biyo bayan sayar da wasu kadarorin gwamnatin jihar a dai dai lokacin da ya ke shirin sauka daga karagar mulki, Ganduje ya bukaci zababben gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf da ya tambayi ubangidansa (Rabiu Musa Kwankwaso) akan yadda gwamnatin sa wadda ya rike mukamin mataimakin gwamna ta sayar da wasu kadarori.

Wadannan kalamai sun biyo bayan sanarwar da gwamnati mai jiran gado ta yi, wanda ya gargadi duk wadanda suka sayi irin wadannan kadarori da kuma filaye da su kaucewa fara aiki a cikin su, domin da zarar sun shigo za su duba yadda aka sayar da filayen da kuma gidajen.

Ganduje ya ce sayar da kadarorin gwamnati ba wani sabon abu bane, domin kuwa su suka kawo shirin Kano lokacin Kwankwaso na matsayin gwamna, kuma sun sayar da gidaje da dama ga ‘yan siyasa da kuma ma’aikata.

Gwamnan mai barín gado ya ce, idan Kwankwaso ya karyata shi, zai je gidan rediyo domin gabatar da shaidar da ke nuna irin gidajen da suka sayar lokacin ya na masa mataimakin gwamna.

Ganduje ya  ce ba laifi bane sayar da kadarorin gwamnati, kuma ba yau aka fara ba, kana kuma ba za a daina ba, domin ko shi lokacin da ya ke aiki a Abuja, ya zauna a gidan gwamnati wanda daga baya aka sayar masa.

Gwamnan ya ce yanzu gwamnati ta daina gina gidaje ta na bai wa ma’aikata su zauna kamar yadda aka saba yi a shekarun baya, yayin da wadanda ta gina kuma ta sayarwa ma’aikatan dke zama a cikin su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here