Najeriya: Kotu ta kori zababben gwamnan jihar Abia daga jam’iyyar Labour

0
116

Wata babbar kotun tarayya da ke Kano a Najeriya, ta soke dukkan kuri’un da dan takarar jam’iyyar Labour Party (LP) Alex Otti ya samu a zaben gwamna da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris.

Rahotanni sun ce a Abia ne kawai jam’iyyar ta samu kujerar gwamna a zaben 2023.

Kotun ta kuma soke takarar dukkan ’yan takarar da jam’iyyar LP ta tsayar a jihohin Abia da Kano a lokacin zaben.

Kotun ta ce jam’iyyar da ke gudanar da ayyukanta musamman a zaben fidda gwani na jihar Abia da Kano ba ta bi ka’idojin zabe ba.

Don haka Alkalin ya yanke hukuncin cewa “kuri’un da aka kada na dukkan ‘yan takarar da ake tuhuma a jihar Kano da kuma jihar Abia a babban zaben 2023, suna cike da kura-kurai.”

Kwanaki biyu da suka gabata ne dai jam’iyyar Labour ta fitar da sanarwar cewa wani bangare na jam’iyyar na neman soke nasarar da jam’iyyar ta samu a zaben 2023.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here