Martanin EFCC kan kalaman Matawalle

0
118

Hukumar EFCC, mai yaƙi da masu yi wa arzikin ƙasa ta’annati ta mayar da jawabi game da tsokacin da gwamnan jihar Zamfara mai barin gado, Muhammad Bello Matawalle ya yi cewa ya kamata hukumar ta soma duk wani binciken badaƙalar da za ta yi daga kan ma’aikatan Fadar shugaban ƙasa.

Tun farko dai wata sanarwa daga shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa, ta ce an tura wa gwamnonin da ke barin mulki da kwamishinoni gayyata da zarar sun kammala miƙa mulki, domin gudanar da bincike a kansu.

A hirar da ya yi da BBC, Shugaban na EFCC, ya ce ba kasafai suke sanar da irin ayyukan da suke yi ba musamman game da binciken rashawa.

A cewarsa, “masu bincike sun miƙa masa wani rahoto da ya ƙunshi wani ɗan kwangila da aka bai wa biliyoyin kuɗi huɗu, “ya zo ya ce ya samar da kayayyaki ba tare da gabatar da takardu da za su tabbatar da hakan ba, kuɗi ya je ya canja su kuma ya kai wa jami’an gwamnati.”

Abdulrasheed Bawa ya ce abin so ne a ce su soma bincike kan jami’an gwamnatin da ake zargi da za su miƙa mulki na da ƴan kwanaki idan har hakan ta samu.

Sai dai ya ce ba abu ne na sauri ba ganin yadda wasu mutane ke tunanin da zarar wani jami’i na barin gwamnati, ya kamata a kama shi a kai shi kurkuku.

Ya ce “waɗannan shugabanni ne, sun yi nasu ƙoƙarin, idan da wani laifi da aka gani za a gayyaci mutum ya zo ya yi bayani.”

Shugaban na EFCC ya kuma yi bayani game da yarjejeniyar da hukumarsu ta cimma da takwararta ta Saudiyya inda ya ce yarjejeniyar za ta ba su damar yin aiki tare domin yaƙar rashawa.

A cikin wata sanarwa da EFCC ta fitar yau Alhamis, ta ce tana bincikar gwamna Matawalle ne kan zargin karkatar da N70bn da bayar da kwangiloli ba bisa ƙa’ida ba.

“Kuɗin wanda aka samu a matsayin bashi daga wani banki domin aiwatar da ayyuka a sassan ƙananan hukumomin jihar, ana zargin gwamnan ya karkatar da shi ne,” kamar yadda sanarwar ta bayyana.

“Binciken hukumar zuwa yanzu ya nuna fiye da kamfanoni 100 ne suka karɓi wani kashi na kuɗaɗen ba tare da wwata hujja da ta nuna an aiwatar da ayyukan ba a jihar.

EFCC ta ce wasu daga cikin ƴan kwangilolin an gayyace su inda aka yi musu tambayoyi kuma sun yi zargin cewa gwwamnan ne ya tilasta musu mayar masa da kuɗaɗen da suka karɓa daga asusun gwamnati ta hannun masu taimaka masa bayan da suka canja kuɗaɗen zuwa dala.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here