Kungiyar G7 na duba yuwuwar yadda za a tsaurarawa Rasha takunkumi

0
104
Shugabannin kungiyar G7 sun isa birnin Hiroshima na kasar Japan, domin tattaunawa kan yadda za a tsauraran takunkumin da aka kakabawa kasar Rasha, da hakan masana ke ganin zai kasance barazana ga tattalin arzikin kasar China.

Firaministan Japan Fumio Kishida na karbar bakuncin shugabannin daga wasu kasashe shida masu karfin tattalin arziki, a guda daga cikin biranen kasar da ya taba fuskantar harin makaman nukiliya, kuma a yanzu cike yake da abubuwan tunawa.

Shugabanni da suka hada da shugaban Amurka Joe Biden za su yi kokari na tsawon kwanaki uku don samar da hadin kai a kan Rasha da China, inda sau dama maslahar kawance kasashen ba sa samar da mafita.

Shirin warware rikicin diflomasiyya da ya dabaibaye shugaba Biden a yankin Asiya ya ci karo da cikas tun kafin ya bar kasar Amurka, sakamakon takaddamar kasafin kudi na cikin gida da ya tilasta masa soke tsayawa a Papua New Guinea da Australia.

Yunkurin mamayar da Rasha ta yi na watanni 15 a Ukraine, shi ne kan gaba wajen tattaunawa a kai a taron kolin G7 a ranar Juma’a, bayan wani sabon hari ta sama da aka kai a Kyiv da kuma Bakhmut da sauran garuruwan Ukraine.

Amurka da kawayenta sun tura makami zuwa Ukraine domin dakile ci gaban da Rasha ta samu, amma har yanzu ba a kai ga dakatar da kai hare-hare da sojojin Kyiv suka dade suna fafutuka a kai ba.

Ana sa ran shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky zai yi jawabi ga shugabannin kungiyar ta yanar gizo

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here