Wata mata ta farke cikin ’yar makwabta kan zargin karin aure a Kano

0
116

Ana zargin wata matar aure da burma wa ’yar makwabtansu wuka a cikinta a Kano.

Aminiya ta gano cewa matar mai suna Fatima ta dauki wannan mummunan matakin ne a kan yarinyar saboda zargin mahaifin yarinyar da zuga mijinta a yunkurin da yake na karo aure.

Sai dai an bayyana cewa tuni wacce ake zargin ta yi layar zana.

Mahaifin yarinyar, Malam Usman Abubakar, ya shaida wa Aminiya cewa ba ya gida lokacin da lamarin ya faru, sai ganin wasu mutane ya yi sun kawo ta a babur mai kafa uku inda suka neme shi da su tafi asibiti.

“Na dawo daga kasuwa sai na sami wasu mutane a mashin mai kafa uku a kofar gida inda suka nuna min ’yata Sharifa da ke cikin mashin din tare da bayyana min cewa na bi su mu tafi Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano.

“Sun gaya min cewa an sami ’yata a wani kango a unguwar Mariri; Sun gaya min cewa wai wata mata ta caka mata wukar.

“Sun shaida min cewa sun yi kokarin kai ta asibiti amma an ce sai an nemo iyayenta.”

Da yake karin haske game da yadda aka dauke ’yar tasa, Malam Usman Abubakar, ya bayyana cewa matar ta hilaci yarinyar ne da zimmar za ta raka ta unguwa, inda daga nan ta tafi da ita ta yi mata aika-aikar.

“Tun farko ta dauki yarinyar nan da sunan za ta raka ta sayen gawayi, inda ta tafi da ita har tsawon lokaci ba tare da ta dawo da ita ba.

“Lokacin da wasu yara suka sanar da ita cewa Fatima ce ta dauki yarinyar ba ta damu ba saboda sun saba sosai.

“Amma da ta ga an dauki tsawon lokaci yarinyar ba ta dawo ba, sai ta shiga damuwa inda ta aika gidan don sanin ko sun dawo.

“A takaice dai sai da mahaifiyar yarinyar ta aika gidan ya fi sau 10, amma sai a gaya mata cewar ba su dawo ba.

“Ita dai ba ta san halin da ’yarta take ciki ba har sai lokacin da aka kawo ta cikin wannan hali.”

Malam Usman ya kara da cewa iya saninsa babu wani batun neman aure da mijin matar ke yi.

“Ni ban san mijinta yana neman aure ba, zargin ta ne kawai wanda kuma ba shi da tushe ballantana makama,” in ji shi.

Duk kokarin Aminiya don jin ta bakin Kakakin Rundunar ’Yan Sanda na Jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ci tura, bai amsa kiran wayar da aka yi masa haka kuma bai amsa rubutaccen sakon da aka aika masa ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here