Yadda aka kashe ma’aikatan ofishin jakadancin Amurka a Anambra

0
108

Akalla mutum hudu aka kashe a wani hari da aka kai wa ma’aikatan ofishin jakadancin Amurka a kan hanyar Atani zuwa Osamale a Jihar Anambra da ke Kudancin Nijeriya.

A wata sanarwa da mai magana da yawun ‘yan sanda reshen Jihar Anambra DSP Ikenga Tochukwu ya aika wa TRT Afrika, ya bayyana cewa wadanda suka kai harin sun kashe ‘yan sanda biyu da ma’aikatan ofishin jakadancin na Amurka biyu.

“Bata-garin sun kashe jami’an ‘yan sanda biyu da wasu ma’aikatan ofishin jakadancin, suka kuma cinna wa gawarwakinsu da motarsu wuta.

“Ko da maharan suka ga jami’an ‘yan sanda na zuwa wurin, sai suka yi garkuwa da ‘yan sanda biyu da direban mota ta biyun inda suka gudu. Babu wani dan kasar Amurka a cikin kwambar motocin,” in ji sanarwar.

DSP Ikenga ya bayyana cewa tuni jami’ansu suka soma neman sauran jami’an dilfomasiyyan da aka sace a Karamar Hukumar Ogbaru.

Kamfanin dillancin labarai na AP ya ambato ma’aikatar harkokin wajen Amurka na cewa ma’aikatanta a Nijeriya na aiki tare da jami’an tsaron kasar domin bincike kan lamarin.

Hukumar ‘yan sandan ta bayyana cewa za ta yi bakin kokarinta wurin yakar bata-gari a jihar.

Jihar Anambra na daga cikin jihohin kudancin Nijeriya da ake fama da ayyukan ‘yan bindiga wadanda suke kai hari a sassan jihar.

Ko a kwanakin baya sai da wasu ‘yan bindiga suka kai hari a ofishin ‘yan sanda a yankin Ihiala da ke Jihar Anambra inda suka saki wasu da ke tsare.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here