Kungiyar ‘yan tawayen jamhuriyar Nijar ta ajiye makamai

0
125

Wata kungiyar ‘yan tawaye a Jamhuriyar Nijar da ta addabi yankunan da ke kan iyakar kasar da Libya ta ajiye makamai.

Kungiyar, mai suna UFPR, ta bayyana haka ne a taron manema labarai da ta gudanar ranar Litinin a Yamai, babban birnin kasar.

Shugaban kungiyar Mahmoud Sallah ya ce sun dauki matakin ne bayan sun gana da shugaban kasar Mohamed Bazoum.

Ya kara da cewa sun yi nadamar daukar makamai a baya, yana mai shan alwashin daina tayar da kayar baya.

UFPR ta kwashe shekaru uku tana kai hare-haren a arewa maso gabashin kasar.

Sallah ya ce sun kafa ta ne saboda zargin da suka yin a yadda gwamnati ke amfani da albakatun ma’adinan kasar domin biyan bukatun wasu tsirarun mutane.

Sai dai a taron manema labaran na Litinin, ya ce yanzu sun gamsu da yadda ake gudanar da mulki a kasar.

UFPR ta kaddamar da harinta na farko ne ranar 15 ga watan Yunin 2022 a yankin Jado da ke jihar Diffa inda jami’in tsaro na jandarma daya ya rasu yayin da uku suka samu raunuka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here