Kamfanin NNPC zai dawo da aikin laluben man fetur a jihar Borno

0
111

A wata zantawarsa da Jaridar Najeriyar Daily Trust Malam Mele Kyari shugaban kamfanin na NNPC, ya bayyana cewa matakin komawa ci gaba da laluben man a jihar Borno umarni ne na kai tsaye daga shugaban kasa mai barin gado Muhammadu Buhari.

A cewar shugaban na NNPC Mele Kyari nasarar gano man fetur a kogin Kolmani da ke tsakanin jihohin Gombe da Bauchi a watan Nuwamban bara ya karfafa gwiwar kamfanin wajen ci gaba da laluben a tafkin Chadi.

Mele Kyari ya ce gano man man a Kolmani ya taimaka matuka wajen gano wani man a jihar Nassarawa, wannan dalili ya tilasta daura aniyar ci gaba da laluben man na jihar Borno.

Shugaban kamfanin na NNPC ya bayyana cewa za su tsauraran matakan baiwa jami’ansu kariya yayin aikin hakar man na fetur a jihar Borno mai fama da hare-haren kungiyar ta’addanci ta Boko Haram.

Rahotanni sun bayyana cewa tun shekara daya da ta gabata ne, shugaba Muhammadu Buhari ya yi umarnin dawo da aikin laluben man a yankin tafkin Chadi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here