Kotu ta yanke wa mutum uku hukuncin kisa kan satar waya da kamfuta a Ekiti

0
101

Wata Babbar Kotu da ke Ekiti ta yanke hukunci kisa ta hanyar rataya kan mutane uku da ta samu da laifukan fashi da makami.

Masu laifin Omotayo Deji mai shekara 23 da Chidiebere Ifeanyin mai shekara 25 da kuma Bolaji Usman mai shekara 28, an gurfanar da su ne gaban kotu a Janairun 2020, kan laifuka hudu da suka hada da fashi da makami.

Alkali Bamidele Omotoso ya ce abin da suka aikata sun kunshi sace wayoyin mutane da kamfuta da takalma da cajar waya wanda duka aka kiyasta kudin kai naira 186,000.

Mutanen uku a cewar kotun sun yi amfani da makami irinsu ada da katako wajen kai hari da sace wadannan kayayyaki.

Wata sanarwar ‘yan sanda ta ambato ɗaya daga cikin shaidu na cewa suna bacci da misalin 2:30 na dare waɗannan matasa suka kutsa gidansu tare da kwashe musu kayayyaki da kuma yi musu barazana da makaman da suke dauke da su.

Alkali ya nuna gamsuwa da hujojjin da aka gabatar masa, ya same su da laifi tare da umartar a kashesu ta hanyar rataya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here