Home Labarai Wani dan ta’adda ya tarwatsa kansa da bam a Kaduna

Wani dan ta’adda ya tarwatsa kansa da bam a Kaduna

0
108

Lamarin ya faru ne a kan hanyar Ibrahim Haske da ke unguwar Keke a Millenium City a sanyin Safiyar wannan Litinin.

Mutanen da lamarin ya auku a kan idanunsu sun ce, an yi jin karar harbe-harben bindiga da misalin karfe 1 na cikin daren da ya gabata lokacin da jami’an tsaron farin kaya na DSS da sojoji suka dirar wa gidan dan ta’addar da ake zargi.

Mutumin ya tarwatsa kansa ne da bam din bayan ya fahimci cewa, jami’an tsaron sun yi masa zobe.

Rahotanni sun ce, mutumin ya dauki lokaci yana musayar wuta tsakaninsa da jami’an tsaro kafin yanke shawarar kashe kansa da kansa, yayin da aka gano bindiga kirar AK-47 a cikin gidansa da kuma wasu bama-bamai.

Tuni jami’an tsaro suka tafi da matar mutumin da ‘ya’yansa bayan ya kashe kansa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here