An Kashe sojoji 3, an raunata wasu 10 a harin ISWAP

0
110

Sojoji uku ne suka mutu yayin da wasu 10 suka samu raunuka daban-daban a wani harin kwantan bauna da kungiyar ‘yan ta’adda ta ISWAP ta kai wa ayarin motocinsu, yayin da suka fatattaki ‘yan ta’addan a karamar hukumar Abadam ta jihar Borno.

An tattaro cewa sojojin, wadanda harin ya rutsa da su, sun hada da runduna ta 3 da ta 4 ta rundunar hadin guiwa ta kasa da kasa (MNJTF), an kai musu harin ne a ranar Lahadin da ta gabata ta hanyar jefa wa ayarin motocin bam (VBIED), akan hanyarsu ta zuwa sansanin ISWAP da ke Tunbum Reza.

Hakan na zuwa ne a wani rahoton sirri da Zagazola Makama, kwararre a fannin yaki da tada kayar baya a yankin tafkin Chadi ya samu daga manyan majiyoyin tsaro, wanda aka bai wa LEADERSHIP, inda ya bayyana cewa dakarun hadin guiwar sun samu nasarar fatattakar ‘yan ta’addan da su kayi musu kwanton baunar.

Majiyar ta ce daya daga cikin Bam (VBIED) din ya bugi wata motar MRAP mallakar sojojin Jamhuriyar Nijar sai kuma wata mota kirar Hilux.

Majiyoyin sun ce an kashe ‘yan ta’addan da dama a harin da basu yi nasara ba, duk da cewa har yanzu ba a tantance adadin ‘yan ta’addan da aka kashe ba.

“Wannan harin ya zo ne cikin kasa da sa’o’i 24 bayan da sojojin suka dakile wani harin a Arege wanda ya yi sanadin kashe ‘yan ta’addar ISWAP 10 tare da lalata motocinsu guda uku.” Inji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here