Mutum biyu sun yi ba-hayar ƙulli 193 na hodar ibilis a hannun NDLEA

0
124

Jami’an Hukumar da ke Hana sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Najeriya NDLEA ta kama mutum 185 a Abuja da Kano kan laifukan da suka shafi safarar ƙwaya.

A wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na Tuwita, ta ce wasu ‘yan kasuwa biyu da ke tsare a hannunta, kwana uku bayan kama su a filin jirgin saman Abuja, sun yi ba-hayar ƙulli 193 na hodar ibilis.

Haka kuma hukumar ta ce ta samu nasarar ƙwace wasu ƙullin hodar ibilis da aka yi niyyar fasa-ƙwaurinsu zuwa Saudiyya daga Canadana.

Hukumar ta kuma bayyana nasarar kamen da ta yi a fadin wasu jihohin ƙasar cikin makon da ya gabata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here