Mene ne tanadin doka kan zaɓen shugabannin majalisa?

0
102

A watan Yunin 2023 ne ake sa ran rantsar da sabuwar Majalisar Dokokin Najeriya.

Sai dai a yanzu, hankali ya fi karkata ga zaɓen waɗanda za su jagoranci majalisun biyu.

Najeriya dai tana da zauruka biyu a ƙarƙashin Majalisar Dokoki ta Tarayya.

A ɓangaren farko, akwai Majalisar Dattawa mai sanatoci 109, wato mutum uku daga kowacce jiha, sai kuma Babban Birnin Tarayya mai sanata ɗaya.

Yadda ake zaɓen shugabannin majalisa

A ranar farko dai dukkanin zaɓaɓɓun mambobin za su hallara a zauren majalisar, inda a nan za su sha rantsuwar kama aiki.

Da farko, dokar majalisar ta fi bai wa yan majalisun da suke dawowa a karo na biyu ko sama da haka damar neman shugabancin, duk da dai hakan bai haramta wa sabbin ƴan majalisa neman shugabancin ba.

Daga nan ne kuma, sai ɗaya daga cikin zaɓaɓɓun sanatocin zai gabatar da buƙatar zaɓen ɗaya daga cikin takwarorinsa a matsayin shugaba.

Idan dai akwai masu neman kujerar sama da ɗaya, sai magatakardan majalisar ya gudanar da ƙuri’a, inda sanata da ya samu ƙuri’a mafi rinjaye wadda babu tababa, wato biyu bisa uku, ne kaɗai za a bayyana a matsayin wanda ya lashe zaɓen.

A bisa al’ada, batun shugabancin majalisun tarayya shi ne ya fi tayar da ƙura a siyasance, bayan kammala zaɓuka.

Kuma a mafi yawan lokuta, irin shugabannin da aka zaɓa, su ne za su nuna salon yadda dangantaka za ta kasance tsakanin ɓangaren zartarwa da masu yin doka.

Duk da cewa an fi jin amon masu neman muƙamin shugaban Majalisar Dattijai, da kuma na Majalisar Wakilai, to amma akwai sauran muƙamai waɗanda suna da matuƙar muhimmanci kuma ana gogoriyo wajen neman su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here