Babu batun shiyya a kundin tsarin mulkin kasa a mukaman majalisu – Kawu Sumaila

0
116

Hon Kawu Sumaila ya shaida cewa a tsari da tanadi na kunɗin tsarin mulki babu dokar da ta ce dole a ware shugabanci majalisa ga wata shiyya ko ɓangare na ƙasa.

Abin da kundin tsrain mulki ya ce shi ne a zaɓi ɗaya daga cikin ‘yan majalisa ba tare da la’akari da jam’iyya ko addini ko ɓangarensa ba, dama ce da kowa ke da ita.

Kawai ɓangaren zartarwa a kowanne lokaci yana son ya mallaki majalisa ne saboda ita ce ‘ƴar sandansu’, a cewarsa.

Kuma sau tari duk lokacin da ake ce hakan abin ba ya yin nasara, shi yasa a lokuta da dama majalisa ke tutsu ta kori wanda aka sa, idan ɓangaren zartawa ya yi tasiri.

Kullum ɓangare zartwarwa idan ya mallaki majalisa, ana samun matsala a kasa tsakanin ɓangarorin biyu, in ji Kawu Sumaila.

‘Bangaren rinjaye na tasiri sosai’

Dan majalisar ya tuno da majalisa ta bakwai, lokacin da marasa rinjaye suka tabbatar da naɗa wanda suke so.

Ya ce a wannan lokaci an saɓa ra’ayin masu rinjaye, shi ne aka tsayar da Aminu Tambuwal da Emeka Ihedioha, sannan a majalisa ta takwas marasa rinjaye ne suka tsayar da Bukola Saraki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here