Babu makawa sai na zama shugaban kasar Najeriya – Peter Obi

0
123

Dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar LP, Peter Obi, cewa ya zama dole ya zama shugaban kasar Najeriya.

Peter Obi ya bayyana haka ne a taron kaddamar da wani littafi da ya wallafa mai suna ‘Peter Ob: Many Voices, One Perspective’.

An kaddamar da littafin ne da nufin tara kudin daukar nauyin shari’ar da ya shigar da kara kalubalantar nasarar shugaban kasa mai jiran gado Bola Tinubu a zaben shugaban kasa.

A cewarsa, “Ya zama dole in zama shugaban ƙasa, idan ba yanzu ba, nan gaba.

“Ban kosa ba kuma ban gaji ba, na sadaukar da kaina domin ganin Najeriya ta inganta,” in ji shi a taron da ya gudana a Awka, hedikwatar Jihar Anambra.

Obi wanda tsohon gwmanan jihar ne, ya yi wannan furuci ne kwana biyu bayan Kotun Sauraron Kararrin Zaben Shugaban Kasa ta fara sauraron karar da ya shigar gabanta tare da jam’iyyar LP.

Kalaman nasa kuma na zuwa ne kwana 17 kafin rantsar da Tinubun a matsayin shugaban kasar Najeriya na 16.

Peter Obi, wanda shi da jam’iyyar ke neman a dakatar da ranstar da Tinubu sai kotu ta yanke hukunci, ya ce zai karbi duk hukuncin da kotun ta yanke.

Ya kuma yi kira ga magoya bayansa da su sallama wa duk hukuncin da kotu t yanke ba tare da wata hayaniya ba.

A cewarsa, gwagwarmayarsa ta zama shugaban kasar Najeriya ba za ta kare ba har sai burinsa ya cika.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here