Katsinawa sun soma tattaki daga Damaturu domin halartar bikin rantsar da Dikko Radda

0
109

Wasu matasa Katsinawa mazauna birnin Damaturu a Jihar Yobe, sun fara attaki zuwa Katsina a kan Kekuna domin halartar bikin rantsar da Dokta Dikko Umar Radda a matsayin sabon Gwamnan Jihar Katsina da mataimakinsa, Faruq Lawan Jobbe don nuna kishin kasa.

A tattaunawar da Aminiya ta yi da su a garin Damaturu kafin fara wannan tattaki, sun bayyana goyon baya ga sabon Zababben Gwamnan na Katsina.

Matasan biyu — Sulaiman Halilu mai shekara 33 da kuma Kamilu A. Bala da ake yi wa inkiyar Amanar Dokta Radda mai shekara 29 — duk ’yan asalin Karamar Hukumar Musawa ce da ke jihar ta Katsina.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, matasan biyu Allah ne Ya kaddara zamansu a garin Damaturu na tsawon lokaci.

Aminiya ta tambayi daya daya daga cikin matasan, Sulaiman Halilu kan dalilin wannan tattaki na nuna soyayya da goyon baya ga Dokta Dikko Umar Radda.

Ya bayyana cewar, makasudin wannan tattaki na su gari da gari har zuwa garin Katsina da keken hawa bai wuce abu biyu ba ne.

“Na farko a lokacin zaben share fage na 2022 a jam’iyyar APC aka zabo mana wasu gwarzaye guda uku na farko; Dokta Radda da Abdullahi Aliyu Talban Musawa a matsayin dan majalisar mu na Musawa da Matazu sai kuma na uku Honarabul Mukhtari ’Yan Dutse a matsayin Sanatan mu daga yankin Funtuwa.

“To tun a lokacin muka yi alkawarin cewa in har sun ci zabe za mu yi wannan tattakin na zuwa shaidar rantsuwar gwamnan don nuna goyon bayan mu da kuma murnar mu, mu ka kuma dace dukannin gwanaye namu sun ci zabe.

“Dalili na biyu kuma muna son tabbatar wa al’ummar Katsina cewar ba Dikko Radda ba ne ya yi nasara, a’a nasara ce ta dukannin Katsinawa.

“Don haka muna mika godiyar mu ga gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari da kuma Daraktan Yakin Neman Zaben Dokta Dikko Radda, Ahmed Musa Dan Giwa da Babanmu, Sanata Abu Ibrahim da Shugaban kungiyar 13-13, Dauda Kahutu Rarara da dan majalisar mu da sauran mutanen da suka ba da gudunmawarsu su da ta kai ga samun wannan nasara.”

Aminiya ta kara neman jin ko akwai wani tagomashi da matasan suka samu daga wadannan ’yan siyasa har suke martaba su haka?

Sulaiman ya bayar da amsar cewa, “to ai ita Juma’a mai kyau tun daga Laraba ake gane ta.

“Domin a shekarar 2015 lokacin da Masari ya lashe zaben gwamnan Katsina ya jawo shi [Dikko] ya ba shi matsayin Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnatin wato (Chief of Staff).

“Daga baya kuma mai girma Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya nada shi Shugaban hukumar nan mai kula da kanana da matsakaitan masana’antu (SMEDAN), inda ya yi shekara hudu da Shugaban Kasa ya ga cancantarsa sai aka kara masa wata shekara hudu.

“To ana haka ne sai mu al’ummar Jihar Katsina mu ka ga cancantarsa muka ce ya fito neman takarar gwamna.

“Hakan kuwa ya amince ya fito da taimakon Allah Katsinawa suka zabe shi a matsayin gwamna a zaben da ya gudana.

Wakilinmu ya tambayi matasan tsawon lokacin da za su shafe suna wannan tattaki?

Sulaiman ya bayyyana cewa, “sun daukin wa’adin sati guda ne in Allah Ya so kafin dai ranar rantsuwa za su kai ga garin na Katsina cikin hukuncin Allah.

“Kuma akwai wadanda suka taimaka mana da yawan gaske don ganin mun kai ga nasarar wannan tattaki namu da suka hada da kungiyar mu ta Katsinawa Mazauna Damaturu da mutanen gwamna Mai Mala Buni da kuma wasu abokan zaman mu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here