Inaki Pena zai ci gaba da golan Barca zuwa 2026

0
127

Barcelona ta cimma yarjejeniya da Inaki Pena, domin ya ci gaba da wasa a kungiyar zuwa karshen kakar Yunin 2026.

An kuma gindaya yuro miliyan 400 ga duk kungiyar da ke son daukar mai tsaron ragar, idan kwantiraginsa bai kare ba a Camp Nou.

Dan kwallon ya saka hannu kan sabuwar yarjejeniya ranar Talata a Camp Nou a gaban shugaban kungiyar Joan Laporta.

Inaki ya fara kama gola a karamar kungiya, Alicante CF, yana shekara 10 da haihuwa ne Villarreal ta dauke shi.

Shekara biyu tsakani Barcelona ta mallaki dan kwallon, wanda ya koma La Masia da ci gaba da karbar horo a 2012

A kakar 2018/19 ya koma atisaye tare da manyan ‘yan wasan Barcelona, amma bai samu damar tsare raga ba, hakan ya sa aka bayar da aronsa ga Galatasaray a Janairun 2022.

Can a Turkiya ya kama gola karo shida a lik da wasa biyu a Europa League, dukkansu ya fuskanci Barcelona.

Ya koma Camp Nou a karshen kakar bara, wanda ranar 3 ga watan Janairu ya shiga cikin manya ‘yan wasan kungiyar.

Ya fara kama gola a Champions League da Barcelona ta ziyarci Viktoria Plzen cikin watan Nuwamba.

Ya tsare ragar Barcelona a karawa biyu a Copa del Rey a kakar nan da ya fuskanci Intercity da kuma Ceuta dukka a waje.

Mai shekara 24 na fatan buga wasan farko a Camp Nou a matakin mai tsaron ragar Barcelona.

Watakila Barcelona ta saka shi a fafatawar La Liga idan ta lashe kofin bana da wuri, domin ya fara samnun kwarewa a gasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here