Gidajen rediyo na yajin aiki a Chadi saboda rashin wuta

0
124
Kungiyoyin kafafen yada labaran rediyo na Chadi sun fara wani yajin aiki na kwanaki biyu domin nuna rashin jin dadin su da karancin man fetur da iskar gas tare da kuma tsadarsu. 

Kungiyar kafofin da ake kira URPT ta dakatar da ayyukan kafofinta baki daya kamar yadda shugaban kungiyar Mekondo Sony ya bukaci hukumomi su dauki mataki akai, a yayin zantawarsa da Sashen Faransanci na RFI.

Bamu da mai a tashoshin sayar da shi. Kafofofin rediyo ba za su iya aiki ba, har ma da mu baki daya.  Ana azabtar da ma’aikata baki daya, domin ko wurin aiki ba ma iya zuwa.

Yanzu haka wasu gidajen rediyo da ofisoshi na amfani da man dizil ne saboda rashin wutar lantarki.

Wannan abu ne mai wahala, saboda haka muka kira yajin aiki na kwanaki 2 domin janyo hankalin hukumomi da su bada tallafi akan makamashi ga gidajen rediyo

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here