Sojojin Majalisar Dinkin Duniya 7 sun jikkata a Mali

0
145

 

Cikin sanarwa da rundunar MINUSMA ta fitar ta shafukan sada zumunta yanzu haka sojojin na samun kulawa a wani asibiti ba tare da karin bayani kan yanayin da suke ciki ba ko kasar da suka fito.

Bam din ya tashi ne a lokacin da ayarin motocin ke kan hayarsa ta zuwa kauyn Douentza dake arewacin kasar.

Rundunar ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce an kai makamaita hare-hare kan dakarunta har sau shida a cikin wannan shekara a tsakiyar Mail, dake fama da kungiyoyi masu ikirarin jihadi.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here