Kusan mutane dubu 10 sun kwarara cikin Afrika ta tsakiya daga Sudan

0
107
Hukumomin Majalisar Dinkin Duniya da suka ziyarci garin da ke kan iyakar Jamhuriyar Tsakiyar Afrika sun bayyana cewa, kimanin mutane dubu 9 da 700 ne suka tsallako cikin kasar daga Sudan kuma ana dakon adadin ya zarta haka nan kusa.

Kashi daya bisa uku na wannan adadi ‘yan asalin Jamhuriyar Tsakiyar Afrika ne, yayin da ‘yan uwansu da abokan arziki suka tarbe su.

Sai dai baki daga cikinsu, sun kafa tantunan wucen-gadi a kusa da garin na Am Dafok da ke kan iyakar Sudan da Afrika ta Tsakiya.

Hukumomin Majalisar Dinkin sun ce yanzu haka suna kan tattaunawa da wani minista wanda zai yanke shawara a madadin gwamnatin kasar game da wurin da za a tsugunar da mutanen.

Garin na Am Dafok na yawan fama da matsalar ambaliyar ruwa, yayin da ake shirin shiga lokaci na damuna a cikin wannan wata, lamarin da ya sa ake fargabar makomar mutanen da suka guje wa yakin Sudan.

Ana fargabar barkewar cututtuka da dama musamman Malaria da kuma fuskantar matsalar karacin abinci a wannan yanki, yayin da Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ke kokarin samar wa mutanen da gidan-sauro domin takaita kamuwa da cutar ta Malaria.

Ana ganin cewa, Jamhuriyar Tsakiyar Afrika ba tudun-mun-tsira ba ne ga mutanen saboda yadda ita ma ke fama da nata tarin matsalolin kuma sama da rabin ‘yan kasar na cikin hali na bukatar agaji.

Kasar ta yi fama da yakin basasa na tsawon shekaru, abin da ya sa ta ci gaba da zama a jerin kasashen duniya mafi fama da talauci.

Majalisarz Dinkin Duniya ta ce, kimanin mutane dubu 120 na cikin bukatar agajin abinci a kasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here