Real Madrid za ta dauki Bellingham kan yuro miliyan 100

0
117

Real Madrid na shirin daukar dan kwallon tawagar Ingila, mai taka leda a Borussia Dortmund, Jude Bellingham kan yuro miliyan 100.

Mai shekara 19, wanda ya koma Dortmund daga Birmingham City a Yulin 2020, yana daga cikin ‘yan wasan da suka taka rawar gani a Ingila a gasar kofin duniya a Qatar a 2022.

Real ta shirya sayen dan kwallon kan kudi da ya kai yuro miliyan 100, amma kungiyar Bundesliga na sa ran sayar da shi kan yuro miliyan 150.

Ana ta alakanta Bellingham da wasu manyan kungiyoyin Turai da cewar zai koma taka leda a karshen kakar nan.

Real tana da tabbacin za ta kulla yarjejeniyar daukar dan wasan nan gaba, wanda bai amince ya sabunta kwantiragin ci gaba da taka leda a Dortmund ba.

Manchester City ma na fatan sayen dan kwallon idan aka kammala kakar nan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here