Hukumar tsaron sirri ta Amurka ta hana wani magajin gari musulmi shiga fadar White House

0
100

Hukumar Tsaro ta Sirri ta Amurka ta dakatar da wani magajin gari na Prospect Park na New Jersey wanda yake Musulmi ne, daga halatar wani bikin karamar sallah da aka shirya shi bayan sallar a Fadar White House tare da Shugaba Joe Biden.

Jim kadan kafin Magajin Garin Mohamed Khairullah ya isa Fadar White House don bikin sallar a ranar Litinin 1 ga watan Mayu, sai aka kira shi daga fadar ana sanar da shi cewar hukumar tsaron sirrin ba ta tantance shi ba.

“Don haka ba zai iya shiga wajen taron ba inda Biden ya gabatar da jawabai ga daruruwan bakin da suka halarta, a cewar Kungiyar Hadin kai na American-Islamic na New Jersey, CAIR-NJ.

Mai magana da yawon Hukumar Tsaro ta Sirri ta Amurkan Anthony Guglielmi ya tabbatar da cewa an hana Khairullah shiga Fadar White House amma bai bayyana dalilin hakan ba.

“A yayin da muke ba da hakuri kan rashin dadin da wannan abu zai jawo, muna sanar da cewa ba a bar magajin garin shiga Fadar White House ba a wannan yammacin,” Guglielmi ya fada a cikin wata sanarwa.

“Ba za mu iya kara yin tsokaci a kan dalilai da hanyoyin da muke bi wajen aiwatar da ayyukanmu na tsaro a Fadar White House ba.”

A watan Janairu ne aka sake zabar Khairullah a matsayin magajin gari a karo na biyar.

‘Ba za a lamunci haka ba’

Shugaban kwamitin CAIR-NJ Selaedin Maksut, ya kira wannan lamari da wanda “ba za a taba lamunta ba kkuma cin mutunci ne.”

“Idan irin wadannan abubuwa na faruwa ga manyan mutane masu daraja na kwamitin hadin kan Musulmai Amurkawa kamar Magajin Gari Khairullah, to ya kamata a dasa ayar tambaya kan: me yake faruwa ga Musulman da ba su ma da irin damar da magajin gari ke da ita? A cewar Maksut.

Khairullah, wanda ya taba yin ayyukan agaji a Syria da Bangladesh, hukumomi sun taba tsayar da shi suka tuhume shi a babban filin jirgin sama John F. Kennedy da ke New York har tsawon awa uku kan ko ya san wasu ‘yan ta’adda, a cewar Dina Sayedahmed, mai magana da yawun kungiyar CAIR-NJ.

Fadar White House ta ki cewa komai kan batun.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here