Kwamishinan Zaben Adamawa Hudu Ari ya shiga hannun ‘Yan sanda

0
143

Cikin wata sanarwa ranar Talata mai magana da yawun rundunar Muyiwa Adejobi, ya ce Yunusa-Ari na hannun ‘yan sanda.

Da ma Sufeto-Janar na ‘yan sandan Najeriya Usman Baba Alkali ya ba da tabbacin kamawa tare da gudanar da binciken duk wadanda ke da hannun a batun siyasar na Adawa idan ya kama harda gurfanar da su gaban kuliya.

A ranar 20 ga watan Afrilu shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da dakatar da jami’in har sai an kammala binciken da ‘yan sanda ke yi.

Rudani

A ranar 16 ga watan Afrilu Yunusa-Ari ya haifar da cece-kuce a kasar bayana da ya ayyana Aisha Binani Dahiru ta jam’iyyar APC a matsayin wacce ta lashe zaben gwamna da aka sake a wasu runfuna tun kafin kammala tattara sakamakon zabe.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here