‘Yan bindiga sun kashe mutum 40 a jihohin Kebbi da Zamfara

0
120

Akalla mutum 40 ‘yan bindiga suka hallaka a kauyukan da ke jihohin Kebbi da Zamfara a wani harin da suka kai a daren jiya Lahadi, inda kuma mutane da dama, suka samu munanan raunuka.

An ruwaito cewa, ‘yansandan kwantar da tarzoma shida, na daga cikin mutane 36 da ‘yan bindigar suka kashe a kauyen Dan Umaru da ke Zuru cikin jihar Kebbi.

Wasu mazauna kauyen sun ce, an bizne mutane 27 da harin ya rutsa da su.

Bugu da kari, ‘yan bindigar sun kuma yi awon gaba da dubban mutane tare da sace daruruwan Shanu a wasu kauyukan da ke makwabtaka da kauyukan da suka kai harin.

Sai dai, mahukuntan ‘yansanda a jihohin na Kebbi da Zamfara har yanzu ba su fitar da wata sanarwar kan kai harin ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here