Buhari ya halarci faretin sojoji da ke zaman na bakwana a gare shi

0
132

Faretin ya gudana ne a babban filin taro na Eaggle Square da ke birnin Abuja, wanda aka fara shi damisalin karfe 10 na safiyar wannan Alhamis, jim kadan bayan isar shugaban Najeriyar sanye da kayan sojoji, tare da shugaban ma’aikatan fadar gwamnatinsa Farfesa Ibrahim Gambari.

Sauran manyan kusoshin gwamnatin da suka halarci taron faretin dakarun Najeriyar fiye da dubu 1 sun hada da, hafsan hafsoshin tsaron Najeiya Janar  Lucky Irabor, da hafsan rundunar sojojin kasa Laftanar Janar Faruk Yahya, da kuma babban Sifeton ‘Yan Sandan Najeriya Usman Baba, da sauran manyan mukarrabai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here