Jamhuriyyar Nijar ta kwaso ‘yan kasarta 42 daga Sudan

0
122

Mutum 42 ‘yan Jamhuriyyar Nijar da aka kwashe daga Sudan sun isa kasarsu lafiya a ranar Laraba.

Ministan Harkokin Wajen Nijar Hassoumi Massaoudou ne ya wallafa hakan a shafinsa na Twitter.

Mr Massaoudou da Jakadan Faransa a kasar Sylvain Itté ne suka tarbe su a filin jirgin saman Diori Hamani da ke birnin Yamai.

Hukumomin Nijar sun yaba wa kasar Faransa, wadda suka ce ita taimaka wajen kwaso mutanen.

Tun bayan da yaki tsakanin dakarun gwamnati da dakarun RSF da ba na gwamnati ba ya yi tsanani a Sudan, kasashen duniya suka fara kokarin kwashe al’ummarsu daga kasar.

“‘Yan uwa da abokan arzikin mutanen da aka kwaso din sun cika da farin cikin ganin dangin nasu sun isa gida lafiya, wadanda aka kai su a wani jirgin soji daga kasar Djibouti,” kamar yadda kafar yada labarai mai zaman kanta a Nijar ActuNiger ta wallafa.

Jaridar ta ambato wani jami’in diflomasiyya a ofishin jakadancin Nijar da ke Khartoum Tahirou Boureima yana cewa “Muna son mika godiyarmu ga hukumomin Faransa da Ma’aikatar Harkokin Wajen Faransa da kuma dakarun faransa da ke Djibouti kan kulawar da suka nuna mana a yayin kwaso mutanenmu.”

Hukumomin Nijar din sun ce an samu nasarar kwaso mutanen cikin yanayi mai kyau.

A ranar Litinin 24 ga Afrilu Majalisar Dinkin Duniya ta ce rikicin kasar Sudan ya yi sanadin mutuwar mutum 427 tare da jikkata mutum 3,700.

Wane hali kuma ‘yan Nijeriya ke ciki?

A hannu guda kuma makwabciyar Nijar din Nijeriya ta ce ta fara kwaso ‘yan kusan 3,500 da suka makale a Sudan, wadanda mafi yawan su dalibai ne, kuma tana hakan ne ta hanyar kai su Masar da mota sannan a wuce da su gida a jirgi

Mai magana da yawun Hukumar ba da Agajin Gaggawa ta kasar NEMA, Manzo Ezekiel ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa “An fara kwaso mutanenmu. Motocin bas bakwai tuni suka bar Khartoum zuwa Masar.”

Ministan Harkokin Wajen Kasar Geoffrey Onyeama ya shaida wa manema labarai cewa an yi hayar bas-bas 40 don kwasar ‘yan Nijeriya zuwa Masar, duk da cewa tafiyar daga birnin Khartoum za ta dauki lokaci.

“Akwai nisa sosai. Muna bukatar ‘yan kwanaki don mu kwashe kowa,” ya ce.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here