Barcelona za ta iya yin asarar €55M na kudin-shiga saboda gyara Camp Nou

0
137

Barcelona za ta yi asarar kusan €55m ($60.7 m) na kudin-shigarta sakamakon rufe filin wasanta na Camp Nou inda za a gudanar da gyare-gayre.

Ranar Laraba kafofin watsa labaran Sifaniya sun rawaito cewa kungiyar za ta koma karamin filin wasa Lluis Companys Olympic da ke Montjuic yayin da ake gyara Camp Nou.

Mataimakiyar shugaban Barcelona Elena Fort ta bayyana yadda kwaskwarimar da za a yi wa filin wasan za ta kasance, tana mai cewa za a soma aiki a kakar wasa mai zuwa daga watan Yuni har karshen watan Nuwamba na 2024.

Fort ta ce za su yi amfani da kujeru 49,472 don gudanar da kasuwanci a filin wasa na Lluis Companys Olympic, wanda ke iya daukar ‘yan kallo 54,367.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here