An kwashe ‘yan kasar Turkiyya 1,600 daga Sudan zuwa Ethiopia

0
121

Majiyoyin difilomasiyya sun bayyana cewa an yi amfani da motocin bas wajen kwashe ‘yan kasar Turkiyya 1,600 zuwa Ethiopia daga Sudan, inda ake ci gaba da fafata kazamin rikici tsakanin sojojin kasar da mayakan RSF.

Majiyoyin sun bayyana cewar Ma’aikatar Harkokin Wajen Turkiyya na ci gaba da kokarin ganin ta kwashe ‘yan kasarta daga Sudan ta hanyar amfani da kasar Ethiopia.

Sun bayyana cewar an fara diban ‘yan kasar Turkiyya a motocin bas da ofishin jakadancin Turkiyya a Addis Ababa ya tanada daga iyakar Sudan da Ethiopia zuwa filin jiragen sama na garin Gondar.

Majiyar ta kara da cewa za a fara kai su Addis Ababa, daga nan kuma a dauke su zuwa gida Turkiyya.

Tuni jirgin farko dauke da ‘yan kasar Turkiyya 164 ya isa zuwa garin Addis Ababa daga Gondar.

An kashe akalla mutane 459 yayin da kimanin 4,072 suka jikkata tun daga 15 ga Afrilu da rikici ya barke a Khartoum babban birnin Sudan tsakanin sojojin kasar da mayakan RSF.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here