’Yan bindiga na neman N500m kan kwamishinar hukumar Kidaya

0
134

’Yan bindiga sun yi garkuwa da wata Kwamishinar Kasa, Hukumar Kidaya ta Kasa a Jihar Bayelsa, Misis Gloria Izonfuo ’Yan bindigar sun bukaci a ba su Naira miliyan 500 kafin su sako Misis Gloria, wadda suka yi garkuwa da ita tare da ma’aikatanta guda biyu.

An sace Misis Gloria Izonfuo, wadda tsohuwar shugabar ma’aikatan Jihar Bayelsa ce a Jihar Ribas, ranar Lahadi a hanyarta ta zuwa  yankin Brass na jihar Bayelsa, daga Fatakwal, babban birnin Jihar Ribas.

Maharan sun yi awon gaba da ita ne tare da direbanta da dan aikinta, kamar yadda kakakin ’yan sandan Jihar Ribas, Grace Iringe-Koko ta tabbatar.

Ta ce kwamishinan ‘yan sanda jihar ya tura runduna ta musamman domin ceto mutanen.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here