ECOWAS: Ana taro kan tsaron tekun Yammacin Afirka

0
132

Shugabannin kasashen kungiyar ECOWAS da ke raya tattalin arzikin kasashen Yammacin Afirka na hallara a Accra, babban birnin kasar gana domin gudanar da taro kan tsaron tekun yankin.

Aana gudanar da taron ne ranar Talata karkashin jagorancin shugaban Ghana Nana Akuffo-Ado.

Tuni shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya bayyana aniyarsa ta halartar taron, wanda zai duba kalubalen da kasashen yankin ke fuskanta wurin shawo kan matsalar da ke addabar tekun Guinea da ya hade kasashen yankin.

 

A sanarwar da fadar shugaban kasar ta wallafa ranar Litinin a Twitter, ta ce Shugaba Buhari zai bar Nijeriya ranar Talata domin halartar taron “shugabannin kasashe da gwamnatocin Yankin Tekun Guinea, (GGC) da Shugaba Nana Akuffo-Ado na Ghana zai shugabanta”.

Ta kara da cewa shugaban zai gabatar da jawabi kan “matakan inganta zaman lafiya da tsaro a yakin da ake yi da laifukan da ke da alaka da fashin teku a yankin.”

Ana asarar miliyoyin daloli da gomman rayuka sakamakon fashin teku a yankin Tafkin Guinea abin da shugabannin kasashen ECOWAS ke gani a kamata a dauki mataki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here