Yau Tinubu zai dawo Najeriya bayan ya shafe kwanaki 34 baya kasa

0
125

Ana sa ran yau Litinin, zababben shugaban kasa Asiwaju Bola Tinubu zai dawo kasa Nijeriya bayan ya shafe kwanaki 34 baya kasa.

Tinubu ya bar kasa ne a ranar 21 ga watan Maris, yayin da kwamitin yakin neman zabensa ya bayyana cewa, zababben shugaban ya fita waje ne domin samun hutun hayaniyar zabe da aka gudanar kuma zai jira ranar 29 ga watan Mayu wacce za a rantsar da shi a matsayin sabon shugaban kasa.

A cikin sanarwar da kwamitin APC na yakin neman zaben shugaban ya fitar a watan Maris ya ce, Tinubu ya tafi kasar Faransa hutu sannan kuma zai biya kasar Saudiyya don gudanar da aikin Umrah kafin zuwan ranar da za a rantsar da shi a matsayin sabon shugaban kasar Nijeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here