Farashin shinkafar da ake nomawa a wasu jihohin Arewa zai iya kara tashi

0
284

Masu amfani da Shinkafar da ake nomawa a kasar nan na ci gaba da jin tsoron kara tashin farashinta.

Masu sarrafa ta a kasar nan, sun danganta yuwuwar farashinta yadda ta yi tsada a kasuwannin da ke a cikin kasar.

Farashin buhunta mai nauyin kilo 50 a garin Abuja a yanzu Wanda ya danganta da irin Shinkafar, ya kai daga Naira 38,000 zuwa Naira 43,000, inda wannan farashin ya kai tun 1960 a lokacin da Nijeriya ta samu ‘yancin kanta.

Ana ci gaba da nuna damuwa cewar, mai farashin ya karu, saboda nomanta na rani da za a yi, ba zai iya cike gibin da aka samu a 2022 saboda aukuwar annobar ambaliyar Ruwa.

Bugu da kari, masu sarrafa ta a jihar Kano sun danganta karancinta kan ambaliyar Ruwa da aka sanu a daminar bara, inda hakan ya lalata gonakan Shinkafa a yankunan da ake nomanta.

Bincike a jihar ya nuna cewa, duk da sayar da ita da aka yi kan farashi mai tsada, an samu karancinta a kasuwannin da ake sayar da ita.

Hakazalika, bincike ya nuna cewa, buhunta mai cin kilo 100, ana sayar da ita kan Naira 25,000, sabanin yadda ake sayar da ita  daga Naira 18,000 zuwa Naira 19,000 a shekarar da ta wuce.

Wani dilanta a karamar hukumar Kura da ke a jihar Kano Malam Shehu Buba ya ce, akasarin kamfanoin da ke sarrafa ta a jihar sun tara ta da yawa.

Lamarin ma haka yake a jihar Benuwe, inda masu sarrafa ta suka bayyana tashin farashin Shinkara da ake nomawa a ckin jihar, duk da karancinta da ake fuskanta.

An ruwaito cewa, a kakar yin girbin shekarar da ta wuce, ana samun babban buhunta kan Naira 30,000, inda bayan wattani sun ci gaba farshinta ya kai Naira 35,000, daga baya kuma farshinta ya kara tashi zuwa Naira 37,000.

Bugu da kari a jihar Neja, gasar da ke akuwa a tsakanin amsu sarrafa Shinkafar a jihar, na kara janoyo karancin ta.

Misali, Buhunta mai nauyin kilo 100 a yanzu ana sayarwa kan Naira 22,000, sabanin yadda a shekarar data wuce, aka sayar da shi kan Naira 16,000

Wani mai sarrafa Shinkafar mai suna, Ibrahim Adamu ya sanar da cewa, a shekarun baya yana sayen Buhunhuna 10,000 Shinkafar wacce kuma yake sarrafa ta ya kai kasuwa don sayarwa.

“A shekarun baya yana sayen Buhunhuna 10,000 Shinkafar wacce kuma yake sarrafa ta ya kai kasuwa don sayarwa.”

“A shekarun baya yana sayen Buhunhuna 10,000 Shinkafar wacce kuma yake sarrafa ta ya kai kasuwa don sayarwa.”

Sai dai, Ibrahim ya bayyana cewa, a yanzu yana iya sayen Buhunhuna 2,300 ne kacal na Shinfar ta cikin gida, saboda yadda ta yi karanci matuka, inda ya kara da cewa, a bana farashinta ya yi tsada sosai.

A cewarsa, a shekarun baya farashin Buhunta mai nauyin kilo 100, ana sayar da shi daga Naira 14,000 zuwa Naira 16,000, amma a yanzu farshinsa ya kai har Naira 22,000.

” A yanzu yana iya sayen Buhunhuna 2,300 ne kacal na Shinfar ta cikin gida, saboda yadda ta yi karanci matuka, inda ya kara da cewa, a bana farashinta ya yi tsada sosai.”

Ibrahim ya danganta tashin farashin nata kan annobar ambaliyar ruwan sama da aka samu a bara a wasu gonakan da ke a cikin jihar.

” A shekarun baya farashin Buhunta mai nauyin kilo 100, ana sayar da shi daga Naira 14,000 zuwa Naira 16,000, amma a yanzu farshinsa ya kai har Naira 22,000.”

Wani daga cikin masu sarrafa Shinkafar a jihar  mai suna Yazid Adamu ya sanar da cewa, kafin karancin kudi a kasar nan, masu sarrafa ta sun fuskanci kalubale wajen sayen ta agun manoma, musamman manoman da suka ke a kauye wadanda suka fi a basu kudi a hannu kafin a sayi Shinkafar ta su.

Ya ce, amma muna sa ran daga  watan Yuni zuwa  Juli, Shinkar za ta kasance a wadace.

Hakazalika a jihar Taraba, wani karamin dan kasuwa a kasuwar  sayar da hatsi ta Mutum biyu mai suna Awwal Mutumbiyu ya bayyana cewa,  ana sayar da Buhu daya daga kan Naira 20,000  zuwa  Naira 22,000.

Ya kara da cewa, Farashin magungunan feshi ya karu, inda a yanzu, ake sayar da Buhu daya na takin zamani kan Naira 25,000, inda hakan ya kara janyo tashin farashin na shikafar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here