Manchester United ta kara azama wajen neman Osimhen

0
164

A wannan kaka Osimhen ya ci kwallaye 26 daga cikin wasanni 31 da ya buga wa Napoli a dukkan gasa.

Har yanzu dai Napoli ba ta fara tattaunawa kan batun sabon kwantiragi tsakaninta da dan wasan na Najeriya ba, wanda saura shekaru biyu ya rage ya kare.

A shekarar 2020 ne Napoli ta sayi  Osimhen a kan kudi fam miliyan 70 daga kungiyar kwallon kafa ta Lille.

Ana rade radin cewa Napoli na jinkirta kulla sabon kwantiragi da dan wasan ne saboda zawarcinsa da Manchester United take yi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here