Yadda dawo da tsoffin takardun kudi ya kara bunkasa kasuwar hatsi a jihar Katsina

0
331

Sake dawo da yin amfani da tsaffin takardun kudi da bankunan kasuwanci suka yi, hakan ya kara habaka kasuwannin da ake hada-hadar sayar da hatsi a jihar Katsina.

Wattani uku da suka gabata, karancin kudi ya janyo shafar farashin hatsi a kasuwanin da ke a cikin jihar ta Katsina.

Har ila yau, an ruwaito cewa, abokan cinikayya a jihar wasu sun fi son su sayi hatsin da kudinsu wasu kuma sun fi son su tura wa masu sayar da hatsin kudin ta hanyar tura masu kudi ta banki, inda tura kudin son sayen hatsin ya fi tsada.

Bugu da kari, rahotanni sun nuna cewa, kafin umarnin na babban bankin Nijeriya CBN, masu hada -hadar sayar da hatsin a ksauwanin jihar, na sayen misali Masara kan Naira 21,000 idan man  sayen hatsin zai biya kudi kai tsaye, inda in kuma zai tura ta banking ne, za a sayar masa kan Naira  for cashless 18,000 duk abin haka yake akan sauran amfanin gona kmar su Wake da Waken Soya da kuma Alkama.

A cewar wani dan kasuwar da ke sayar da hatsin a jihar Shehu Halliru, umarnin da babban bankin Nijeriya CBN ya  bai wa bankun kasuwanci na ci gaba da amfani da takardun kudin har zuwa watan Disambar wannan shekarar, hakan ya kara bunkasa kasuwancin na hada -hadar hatsin a jihar.

Halliru ya ci gaba da cewa, “Mu ‘yan kusuwar mune muka fi shan wahala domin sai mun samo kudi domin mu biya bukatar manoman da ke sayar da hatsin kafin mu siya.”

“Umarnin da babban bankin Nijeriya CBN ya  bai wa bankun. “

kasuwanci na ci gaba da amfani da takardun kudin har zuwa watan Disambar wannan shekarar, hakan ya kara bunkasa kasuwancin na hada -hadar hatsin a jihar.

Ya ci gaba da cewa,” A wani lokacin muna samo kudaden ne da matukar tsada, kafin mu sayi hatsin, inda ya ce, akasarin manoman, ba su da asusun ajiya a bankuna “

A cewar Halliru, amma bisa wannan umarnin na babban bankin Nijeriya CBN, sanar ta mu da dawo a hankali

Hakazalika, suma manoman da ke jihar sun bayyana cewa, samun wadatattun kudaden a kasuwannin jihar, ya kara taimaka wa wajen hada -hadar kasuwancin na hatsin a cikin sauki.

Dawo da amfani da tsaffin takardun kudi, samun wadatattun kudaden a kasuwannin jihar, ya kara taimaka wa wajen hada -hadar kasuwancin na hatsin a cikin sauki. “

Wani manomi a jihar mai suna Muhammad Hambali Doro ya bayyana cewa, umarnin na babban bankin Nijeriya CBN, ya taimaka wajen kara bunkasa hada -hadar kasuwancin na hatsin a jihar.

A cewar Muhammad “A yanzu mun kara samun kwarin guiwa a kasuwannin ganin cewa, an samu wadatattun tsaffin takardun kudaden kai tsaye ba tare da sai an tura kudaden ta hanyar asusun banki ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here