‘Yan bindiga sun harbe ‘yan sanda biyar da ma’aurata a Imo

0
128

Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba sun kashe jami’an ‘yan sanda biyar da wasu ma’aurata da ke jihar Imo a Kudancin Najeriya.

Jaridar PR Nigeria a kasar ta ruwaito cewa ‘yan bindigar sun gudanar da wannan danyen aikin ne a kwanar Okpala da ke Karamar Hukumar Ngor Okpala a ranar Juma’a.

Wannan lamarin na zuwa ne kasa da wata daya bayan ‘yan bindigar sun yi kwanton bauna inda suka kashe jami’an hukumar civil defence biyar a yankin.

Duk da cewa ba a san sunayen ‘yan sandan da aka kashe ba, amma an bayyana cewa ma’auratan da aka kashe su ne Mista Chinaka Nwagu da mai dakinsa wadanda ‘yan asalin garin Amankwo Okpala ne.

‘Yan sandan da aka kashe sun tashi ne daga ofishin ‘yan sanda da ke Abo Mbaise inda suka je kwanar Okpala domin su ci abinci, inda a nan ‘yan bindigan suka rutsa su. Suna cikin cin abincin ne ‘yan bindigar suka bude musu wuta.

Wani wanda ya shaida lamarin ya bayyana wa PR Nigeria cewa ‘yan sanda uku aka kashe a wurin, sai biyu suka gudu zuwa wani wurin cin abinci, sai maharan suka bi su har can suka kashe su.

Bayan haka suka harbe ma’auratan wadanda ke da wurin cin abincin sakamakon sun boye ‘yan sandan a shagonsu.

Rundunar ‘yan sandan Nijeriya dai ba ta ce komai ba dangane da wannan lamarin.

Mun kira mai magana da yawun ‘yan sandan Nijeriya reshen Jihar Imo domin jin karin bayani amma bai daga waya ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here