Hatsarin kwale-kwale ya kashe mutum biyar a Kano

0
112

Akalla mutum biyar ne suka rasu sakamakon hatsarin kwale-kwale da ya rutsa da su a Jihar Kano da ke arewacin Nijeriya.

Mai magana da yawun ‘yan sandan Nijeriya reshen Jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya tabbatar wa TRT Afrika aukuwar lamarin.

Ya bayyana cewa wasu matasa takwas ne suka je kogin Panshekara inda suka hau kwale-kwale, biyar daga ciki suka rasu.

“A ranar 21 ga wata, misalin karfe bakwai da minti arba’in da biyar, wasu matasa su takwas da ‘yan unguwar Fagge da Dala suka je kogi na Panshekara inda suka hau kwale-kale.

“A yunkurin tsallaka wannan kogi, kwale-kwale ya kife da mutane bakwai a ciki wadanda suka fada cikin ruwa,” in ji SP Kiyawa.

Ya kara da cewa an ceto mutane biyu, amma biyar sun mutu kuma an gano gawarwakinsu.

Ya ce an kai su asibitin Murtala inda a nan aka tabbatar da sun rasu.

Kazalika ya ce yanzu haka ana gudanar da bincike a kan wannan lamarin.

Ana yawan samun hatsarin kwale-kwale a Kano da wasu sassa na Nijeriya.

Ko a shekarun baya sai da kwale-kwale ya kife a Karamar Hukumar Bagwai da ke Kano inda kusan mutum 30 suka rasu.

Haka ma a Jihar Kebbi kwale-kwalen ya kife a kwanakin baya inda sama da mutum 100 suka rasa rayukansu.

Ana alakanta kifewar kwale-kwale a Nijeriya da yawan lodi da kuma rashin kula da su kansu kwale-kwalen.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here