Kylian Mbappe ya sa PSG ta kara jin kanshin Kofin Ligue 1

0
142

Kylian Mbappe ya zura kwallo biyu a wasan da Paris Saint-Germain ta kawar da Angers sannan ta jaddada matsayinta a yunkurin daukar Kofin Ligue 1 karo na 11.

An tashi wasan ne da ci 2-1

Mbappe ya zura kwallon farko a ragar Angers a minti na 10 da soma wasa bayan Juan Bernat ya wurgo masa ita.

Ya sake cin kwallo yayin da Lionel Messi ya aiko masa da ita.

Sada Thioub ya ci wa Angers kwallo guda.

Wannan nasara ta bai wa PSG maki 75 jimilla kuma tana gaban Marseille – wadda za ta fafata da Lyon ranar Lahadi – da maki 11 inda take da sauran wasa shida.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here