Home Labarai Tsaro Sojoji sun kashe ‘yan ta’adda, sun kubutar da fararen hula 468 a...

Sojoji sun kashe ‘yan ta’adda, sun kubutar da fararen hula 468 a Najeriya

0
132

Daraktan labarai na ma’aikatar tsaron, Musa Danmadami ne ya bayyana haka ga wani taron manema labarai ranar Alhamis a Abuja.

Manjo Janar Danmadami, ya ce sojojin Najeriyar sun kuma cafke ‘yan ta’adda, tare da wasu masu taimaka musu akalla 122 cikin makwanni  biyun da suka gabata.

Ya kara da cewa, 30 daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su da aka ceto suna asibiti bisa raunuka da suka samu, a yayin da aka sada sauran kuma da iyalansu.

A yankin Arewa maso gabashin kasar, Janar Danmadami ya ce ya ce dakarun rundunar Operation Hadin Kai  sun kai samame sansanonin ‘yan Boko Haram da ISWAP a tsaunuka da dazuka, inda suka kashe ‘yan ta’adda 24 tare da kame 40,  da wasu masu taimaka musu da bayanai.

A cewarsa, jimillar ‘yan ta’addan Boko Haram da na ISWAP 501 da iyalansu ne suka mika wuya , cikin su maza 60, mata baligai 176 da yara 266.

Dakarun na Najeriya sun kuma kwace dimbim makamai daga ‘yan ta’addan da suka hada da bindigogi kiraar AK 47 da 49 guda 14, da manyan bindigogin atilari 4.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here