Sallah: Yadda maza ke cin kasuwar yi wa Mata kunshi da kwalliya a Kano

0
95

A wannan rahoton na musamman, Aminiya ta gano wasu maza a Jihar Kano da ke cin kasuwa lokacin sallah ta hanyar cancada wa mata ado da kunshi da gyaran gashi.

A tattakin zuwa Kasuwar Sabon Gari, mun tattauna da guda daga cikin matasan da ake yi wa lakabi da Mai Kyau da ya yi suna wajen yi wa mata musamman ma sanannu a jihar da kasa baki daya, gyaran gashi, da kwalliya.

Aminiya ta tuntubi matashin don jin yadda aka yi ya fara wanann sana’a, a Kano.

“Farkon zuwa na Kano ba kwalliya na fara ba, waka nake yi ta gambarar zamani da Hausa (Hausa Hip-hop) a shekarar 2000 don har kundin waka na fitar.

“A Saudiyya aka haife ni kuma mu wannan ba wani bakon abu ba ne a al’adarmu gaskiya.

“Daga baya na koma saka farce, da kwalliya, da gashin ido, lokacin wani ubangidana mai suna Abeg wanda Kirista ne.

“Na ji dadin mu’amala da shi saboda ba ya nuna min bambamcin addini ko harshe. Daga baya na fara koyon kitso har na zo na bude gurin gyaran gashi nawa na kaina har guda biyu.

Ni duk wata suka ba ta damuna

Mai Kyau ya ce wata tsangwama ko nuna kyama ba sa damunsa domin shi dan gayu ne da ke koyi turawan Amurka.

“Ni fa dan gayu ne da ke kallon yadda Nigogin Amurka ke bude wuraren daga karfe, wajen aski da gyaran gashi.

“Kuma hakan na burge ni a matsayina na Niga, kuma mai sana’a ba mai zaman banza ba. Shi ya sa na fara Salon (wurin gyaran jiki) har fitattun mata (Cele) abin ya burge su suka fara zuwa ina yi musu.

“Sunana ya bazu don yanzu haka ba a iya Najeriya nake da  kwastamomi ba, suna na ya bazu a ko’ina a duniya har kasashe da dama sun sanni, kusan kasashe biyar ina hulda da su, akwai Saudiyya, Chadi, Kamaru, Aljeriya, Nijar da sauransu.

“Wani lokacin suna ba ni aiki na yi musu hular gashi, ko kitso, su kuma ’yan Kamaru suna zuwa kitso, a haka wani ya ga aikina tunda ba na tallan aikin nawa musamman a soshiyal midiya yana burge su.

Na fi duk matan da ke gyaran gashi a Kano ciniki

Dangane da yanayin ciniki a sallar bana kuwa, Mai Kyau ya ce tun daga shekaru biyu baya cinikinsa bai yi kasa ba, hasalima sunansa kara bunkasa yake.

“Ciniki AlhamdulilLah, kwastamomin karuwa suke daga shekaru biyu baya zuwa yanzu.

“Hakan na da alaka da yadda nake karbar kwastamomina ba na nuna musu kyama kowa nawa ne, da wadanda harshenmu ko addininmu daya ko akasin haka, kowa nawa ne.

“Ni zan iya ce miki ma na fi duk wata mai shagon gyaran gashi ciniki a Sabon Gari, saboda abu ne da ba a saba gani ba a Arewacin Najeriya. Kuma abinda nake yi yana burge mutane fiye da na matan ma.

“Wannan ya haifar min da matsala tsakanina da matan don in dai kai me Salon ne a Kano to a bayana kake.

Dangane da kalubale kuwa Mai Kyau ya ce yama fuskanta bai wuce na budurwarsa da yake kauna da ta yi aure ba, kuma har yau bai daina kaunarta ba “don ba yadda zan yi ne.”

“Ba wai don babu matan da ba sa sona ba ne, ina tsoron matan Najeriya ne, ita din dai kawai nake so”, in ji shi.

Fatansa

Mai Kyau ya ce fatansa bai wuce ya cika da imani ba kamar yadda shi da mahaifansa ke masa addu’a.

Kazalika, Mai Kyau ya ce yana fatan matasan Najeriya za su yi watsi da dabi’ar shaye-shayen miyagun kwayoyi da ta zama ruwan dare a kasar.

Ya kuma ce idan Allah Ya ba shi wata sana’ar zai iya ajiye wannan da yake yi, kasancewar a baya ma ba da ita ya fara ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here